Amos 5:12 - Littafi Mai Tsarki12 Na san irin zunuban da kuke yi, Da mugayen laifofin da kuka aikata. Kuna wulakanta mutanen kirki, Kuna cin hanci, Kuna hana a yi wa talakawa shari'ar adalci a majalisa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”