Allah zai hallakar da waɗanda suke zambatar waɗansu, da waɗanda sukan hana a hukunta wa masu mugun laifi, da waɗanda sukan yanka ƙarya don a hana wa amintattu samun shari'ar adalci.
Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”
Mazaunan duniya kuma, sai su yi ta alwashi a kansu, suna ta shagali, suna a'aika wa juna da kyauta, domin annabawan nan biyu dā sun azabtar da mazaunan duniya.
Sai suka yi ta yi wa manzannin Allah ba'a, suka raina maganarsa, suka yi wa annabawansa ba'a, sai Ubangiji ya husata da jama'arsa don abin ya kai intaha.
Yana magana ke nan, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Ka rufe baki! In kuwa ba haka ba in sa a kashe ka.” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”
Sa'ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Ka tarshe ni ko, maƙiyina?” Iliya ya amsa ya ce, “I, na tarshe ka, gama ka ba da kanka ga aikata mugunta a gaban Ubangiji.
Ebed-melek, bābā, mutumin Habasha, wanda yake a gidan sarki, ya ji labari sun saka Irmiya a rijiya. A lokacin nan, sarki yana zaune a Ƙofar Biliyaminu.
Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta, Ku yi adalci cikin majalisar alƙalanku! Watakila Ubangiji Allah Mai Runduna Zai yi wa sauran da suka ragu na wannan al'umma alheri.