Amos 4:10 - Littafi Mai Tsarki10 “Na aukar muku da annoba irin wadda na aukar wa Masar. Na karkashe samarinku a wurin yaƙi, Na kwashe dawakanku. Na cika hancinku da ɗoyin sansaninku. Duk da haka ba ku komo wurina ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 “Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.
Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.