Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 3:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Hakika Ubangiji ba yakan aikata kome ba, Sai da sanin bayinsa annabawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 3:7
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.


Ubangiji ya ce, “Zan ɓoye wa Ibrahim abin da nake shirin aikatawa?


Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi, Yakan koya musu alkawarinsa.


Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala'ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,


Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.


Bayan wannan na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā, mai kama da ƙaho, ta ce mini, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.”


Zan faɗa maka abin da yake rubuce a littafin gaskiya. Ba wanda zai taimake ni yaƙi da waɗannan, sai dai Mika'ilu shugabanka.


Amma da a ce sun tsaya cikin shawarata, Da sun yi shelar maganata ga jama'ata, Da sun juyar da su daga muguwar hanyarsu, Da mugayen ayyukansu.


To, ka rubuta abubuwan da ka gani, da abubuwan da suke a nan a yanzu, da abubuwan da suke shirin aukuwa bayan wannan.


“Yanzu zan faɗa maka gaskiya. Za a ƙara samun sarakuna uku a Farisa, amma na huɗun zai fi dukansu dukiya. Sa'ad da ya ƙasaita saboda dukiyarsa, zai kuta dukan daularsa ta yi gaba da mulkin Hellas.


“Ku tafi ku yi tambaya ga Ubangiji saboda ni, da jama'a, da dukan mutanen Yahuza a kan maganar littafin nan da aka samo, gama Ubangiji ya yi fushi da muƙwarai saboda kakanninmu domin ba su bi maganar littafin nan ba, har da za su yi dukan abin da aka rubuta mana.”


Ɗaya daga cikin fādawan ya ce, “A'a, ranka ya daɗe, sarki, ai, annabi Elisha ne wanda yake cikin Isra'ila, yake faɗa wa Sarkin Isra'ila maganar da kake faɗa a ɗakin kwananka.”


Domin haka, ba za ka ga hukuncin da yake zuwa a kan Urushalima ba, za a kai ka cikin kabarinka lafiya.’ ” Mutanen kuwa suka mayar wa sarki Yosiya da wannan magana.


sai dai a lokacin busa ƙahon da mala'ika na bakwai zai busa ne, za a cika asirtaccen nufin nan na Allah, bisa ga bisharar da ya yi wa bayinsa annabawa.


“A ranan nan zan naɗa ɗaya daga cikin zuriyar Dawuda ya zama babban sarki, zan kuma buɗe bakinka a tsakiyarsu. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji.”


Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.”


Ana gobe Saul zai tafi wurin Sama'ila, Ubangiji ya bayyana wa Sama'ila.


Ubangiji ya ce mini “Zan duba daga samaniya a hankali kamar yadda raɓa take saukowa a natse da gumin dare a lokacin girbi, hasken rana kuma a yini.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ