A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.
Ku kasa kunne ga wannan, ya ku matan Samariya, Ku da kuka yi ƙiba kamar turkakkun shanu, Ku da kuke wulakanta kasassu, Kuna yi wa matalauta danniya, Kukan umarci mazajenku, Ku ce, “Kawo mini abin sha!”