Amos 3:14 - Littafi Mai Tsarki14 “Ran da na hukunta mutanen Isra'ila saboda zunubansu, Zan hallakar da bagadan Betel. Za a kakkarya zankayen bagaden, Su fāɗi ƙasa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da aka gama duka, sai dukan Isra'ilawa da suka hallara, suka bi cikin biranen Yahuza, suka farfashe al'amudan, suka ragargaza Ashtarot, suka farfashe masujadai da bagadai duka da suke a Yahuza da Biliyaminu, da na Ifraimu da Manassa har suka hallakar da su duka. Sa'an nan dukan jama'ar Isra'ila suka koma garuruwansu, ko wanne zuwa mahallinsa.