Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 2:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ubangiji ya ce, “Mutanen Isra'ila sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun sayar da salihai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta Waɗanda bashinsu bai kai ko kuɗin bi-shanu ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Isra’ila, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun sayar da adalai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 2:6
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sun jefa kuri'a a kan mutanena, Sun sayar da yara, mata da maza, zuwa bauta Don su biya karuwai da ruwan inabi.


Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa'an nan kun sayar da su ga Helenawa.


Allah zai hallakar da waɗanda suke zambatar waɗansu, da waɗanda sukan hana a hukunta wa masu mugun laifi, da waɗanda sukan yanka ƙarya don a hana wa amintattu samun shari'ar adalci.


Ba su yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsa har da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su kasa kunne ba, balle su aikata. Domin wannan Samariya ta faɗi.


Sarkin Assuriya kuwa ya kwashi Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.


“‘Ga shi, na tafa hannuna saboda ƙazamar riba da ka ci, da jinin da ka zubar.


Ta haka kuke hana wa talakawa hakkinsu, kuna kuma ƙin yi musu shari'ar gaskiya. Ta haka kuke ƙwace dukiyar gwauraye, wato matan da mazansu suka rasu, da ta marayu.


Masu sayensu za su yanyanka su, ba za a kuwa hukunta su ba. Masu sayar da su kuma za su yi hamdala gare ni, su ce sun sami dukiya. Makiyayansu kuwa ba su ji tausayinsu ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ