Ina ganinsa, amma ba yanzu ba, Ina hangensa, amma ba kusa ba. Tauraro zai fito daga cikin Yakubu, Kandiri zai fito daga cikin Isra'ila, Zai ragargaje goshin Mowabawa, Zai kakkarya 'ya'yan Shitu duka.
Na san irin zunuban da kuke yi, Da mugayen laifofin da kuka aikata. Kuna wulakanta mutanen kirki, Kuna cin hanci, Kuna hana a yi wa talakawa shari'ar adalci a majalisa.