Amma idan ba ku kasa kunne gare ni ba, ba ku kuwa kiyaye ranar Asabar da tsarki ba, kun kuma ɗauki kaya kun shiga ta ƙofofin Urushalima a ranar Asabar, sai in cinna wa ƙofofin Urushalima wuta. Za ta kuwa cinye fādodin Urushalima, ba kuwa za ta kasu ba.’ ”
Sai Yehowash ɗan Yehowahaz ya ƙwace daga hannun Ben-hadad, ɗan Hazayel, biranen da Ben-hadad ya ci da yaƙi daga hannun Yehowahaz, tsohonsa. Sau uku Yehowash ya ci shi da yaƙi, sa'an nan ya karɓe biranen Isra'ila.
“Gama mutanen Isra'ila sun manta da Mahaliccinsu, Sai sun gina manyan gidaje masu daraja. Mutanen Yahuza kuma sun yawaita biranensu masu garu, Amma ni Ubangiji, zan aika da wuta a kan biranensu, Ta ƙone fādodinsu.”
Sa'an nan Asa ya ɗebo azurfa da zinariya daga dukiyar da take cikin Haikalin, da na fādar sarki, ya aika wa Ben-hadad da su, wato Sarkin Suriya, wanda yake zaune a Dimashƙu, yana cewa,