Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Amos 1:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Ubangiji ya ce, “Mutanen Ammon sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don haɗamarsu ta ƙasa, Suka tsaga mata masu ciki a Gileyad.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Amos 1:13
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta, Gama ta tayar wa Allahnta. Za a kashe mutanenta da takobi. Za a fyaɗa jariranta a ƙasa, A kuma tsage matanta masu ciki.”


“Da yake ya ce al'umman nan biyu, da ƙasashen nan biyu za su zama nasa, ya mallake su, ko da yake Ubangiji yana cikinsu,


Kun shiga uku! Kuna ƙara wa kanku gidaje da gonaki a kan waɗanda kuke da su a dā. Ba da jimawa ba za a ga ba sauran filin da zai ragu ga kowa, ku kaɗai za ku zauna a ƙasar.


Ubangiji ya ce, “Mutanen Dimashƙu sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun zalunci mutanen Gileyad da zalunci mai tsanani.


“Kai ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce, ga abin da Ubangiji Allah ya ce a kan Ammonawa, da a kan zarginsu. “ ‘An zare takobi don kashe-kashe, An goge shi don ya yi sheƙi kamar walƙiya!


Amma sa'ad da Sanballat Bahorone, da Tobiya Ba'ammone, bawa, da Geshem Balarabe, suka ji labari, sai suka yi mana ba'a, suka raina mu, suka ce, “Me kuke yi? Kuna yi wa sarki tayarwa ne?”


“Yanzu kuma ga mutanen Ammon, da na Mowab, da na Dutsen Seyir, waɗanda ka hana Isra'ilawa su kai musu yaƙi sa'ad da suka fito daga ƙasar Masar, su ne mutanen da Isra'ila suka ƙyale, ba su hallaka su ba.


Bayan wannan sai mutanen Mowab, da mutanen Ammon, tare da waɗansu daga cikin Me'uniyawa, suka zo su yi yaƙi da Yehoshafat.


Ubangiji kuwa ya sa ƙungiyar maharar Kaldiyawa, da ta Suriyawa, da ta Mowabawa, da ta Ammonawa su yi gāba da Yahuza, su hallaka su bisa ga maganar Ubangiji, wadda ya faɗa wa bayinsa annabawa.


Sa'ad da ku kuka zo kusa da Ammonawa, kada ku dame su, ko ku tsokane su, gama ba zan ba ku abin mallaka daga yankin ƙasar Ammonawa ba, domin na ba da ita ta zama mallaka ga zuriya Lutu.’ ”


Da mutanen Gebal, da na Ammon, da na Amalek, Da na Filistiya, da na Taya.


A lokacin nan sai Menahem ya hallaka Tifsa da dukan waɗanda suke cikinta, da karkararta tun daga Tirza, domin ba su karɓe shi ba, saboda haka ya hallaka ta, ya tsattsage dukan matan da suke da juna biyu.


Ya kuma kamo mutanen da suke cikin birnin, ya sa su su yi aiki da zartuka, da faretani, da gatura. Ya kuma sa su yi tubula. Haka Dawuda ya yi da dukan biranen Ammonawa. Sa'an nan Dawuda da dukan sojojinsa suka koma Urushalima.


Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?” Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.”


Ya mutanen Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allahnku, Gama zunubinku ya sa kun yi tuntuɓe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ