Za su washe dukiyarki da kayan cinikinki. Za su kuma rurrushe garunki da kyawawan gidajenki. Za su kwashe duwatsu, da katakai, da tarkace, su zubar a cikin teku.
Domin lokacin hallaka dukan Filistiyawa ya yi. Za a datse wa Taya da Sidon kowane taimakon da ya ragu, Gama Ubangiji zai hallaka Filistiyawa Waɗanda suke baƙin teku na Kaftor.
Saboda yawan muguntarka da rashin gaskiyarka cikin kasuwanci, Ka ƙazantar da tsarkakakkun wurarenka. Don haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, Na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suka kallace ka.