7 kuna bauta da kyakkyawar niyya domin Ubangiji kuke yi wa, ba mutane ba.
7 Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba.
Kome za ku yi, ku yi shi da himma kuna bauta wa Ubangiji ne, ba mutum ba,
To, duk abin da kuke yi, ko ci, ko sha, ku yi kome saboda ɗaukakar Allah.
Amma barorinsa suka je wurinsa, suka ce masa, “Ranka ya daɗe, da a ce annabin ya umarce ka ka yi wani babban abu ne, ashe, da ba ka yi ba, balle wannan, da ya ce ka tafi ka yi wanka, ka tsarkaka?”
Kun sani na yi wa mahaifinku barantaka da dukan ƙarfina,
Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku.