15 shirin kai bisharar salama ya zama kamar takalmi a ƙafafunku.
15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku.
Me ya fi wannan kyau? A ga manzo yana zuwa ta kan duwatsu, Ɗauke da albishir mai daɗi, labarin salama. Ya yi shelar nasara, ya ce wa Sihiyona, “Allahnki sarki ne!”
Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!”
Ubangiji Allah shi ne ƙarfina, Ya sa ƙafafuna su zama kamar na bareyi, Ya kuma sa ni in yi tafiya a cikin maɗaukakan wurare.
Amma uban ya ce wa bayinsa, ‘Maza ku kawo riga mafi kyau, ku sa masa. Ku sa masa zobe da takalma,
Ƙafafunki suna da kyau da takalmi, Ke mafificiyar budurwa! Tsarin cinyoyinki kamar aikin gwanin sassaƙa ne.
Kurfanka na baƙin ƙarfe ne da tagulla, Ƙarfinka ba zai rabu da kai ba muddin ranka.”
amma su sa takalmi, kada kuma su haɗa taguwa biyu.