22 Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa.
22 Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi.
Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace a cikin Ubangiji.
su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah.
Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”
Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa.
Sa'ad da aka ji dokar sarki, wadda zai yi a dukan babbar ƙasarsa, dukan mata za su girmama mazansu, ƙanana da manya.”
Sai mata su yi shiru a cikin taron ikkilisiya, don ba a ba su izinin yin magana ba, sai dai su bi, kamar dai yadda Attaura ma ta ce.
Sai ya aika da takardu zuwa dukan lardunan sarki, kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da harshensu, domin kowane namiji ya zama shugaban gidansa, ya kuma zama mai faɗa a ji.
Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya, da hali bangirma tare da matsananciyar kula da zuciya ɗaya, Almasihu kuke yi wa ke nan,
To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a Sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah.