Haka nan ku masu ƙuruciya, ku yi biyayya ga dattawan ikkilisiya. Dukanku ku yi wa kanku ɗamara da tawali'u, kuna bauta wa juna, gama “Allah yana gāba da masu girmankai, amma yana wa masu tawali'u alheri.”
Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.
Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna.
Waɗanda suka riga ni mulki sun nawaita wa mutane. Sun yi ta karɓar abinci da ruwan inabi daga gare su, banda shekel arba'in kowace rana domin abinci da ruwan inabi. Har ma barorin masu mulki sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.
Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”
Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.
Da yake muna tsoron Ubangiji, shi ya sa muke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda muke kuwa, ai, sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin yake a lamirinku.