Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba.
Ga shi kuma, kun dai san irin zamanin da muke a ciki, ai, lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci. Gama yanzu mun fi kusa da ceton nan namu a kan sa'ad da muka fara ba da gaskiya.