To, 'yan'uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha'anin kowane ɗan'uwa malalaci, wanda ba ya bin ka'idodin da kuka samu a wurinmu.
ka yi wa'azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa.
Allah zai hallakar da waɗanda suke zambatar waɗansu, da waɗanda sukan hana a hukunta wa masu mugun laifi, da waɗanda sukan yanka ƙarya don a hana wa amintattu samun shari'ar adalci.
Faɗakarwar da mutumin da ya gogu da al'amuran duniya ya yi ga wanda yake da niyya ya kasa kunne, tamaninta ya fi na zoben zinariya, ko kayan ado da aka yi da zinariya tsantsa.
Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri, Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai, Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.
Ga Saratu kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ɗan'uwanki azurfa guda dubu, shaida ce ta tabbatarwa a idanun dukan waɗanda suke tare da ke, da kuma a gaban kowa, cewa ba ki da laifi.”
domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”