domin ku zama 'ya'yan Ubanku wanda yake cikin Sama. Domin yakan sa rana tasa ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.
Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.
“Duk da haka yawan mutanen Isra'ila Zai zama kamar yashi a bakin teku, Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba. Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’
don ku zama marasa abin zargi, sahihai, 'ya'yan Allah marasa aibu, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya,