Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Afisawa 4:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Jiki guda ne, Ruhu kuma guda, kamar yadda aka kira ku a kan begen nan guda, wanda yake game da kiran nan.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Afisawa 4:4
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin ta gare shi ne dukanmu biyu muka sami isa gun Uba ta hanyar Ruhu guda.


Don haka, ni ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku,


a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,


Amma ga shi, akwai gaɓoɓi da yawa, jiki kuwa ɗaya.


saboda bege ga abin da aka tanadar muku a sama. Kun riga kun ji labarin wannan a maganar gaskiya,


Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.


To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.


muna sauraron cikar begen nan mai albarka, wato bayyanar ɗaukakar Allahnmu Mai Girma, Mai Cetonmu Yesu Almasihu,


duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil'azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,


To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,


Salamar Almasihu kuma tă mallaki zuciyarku, domin lalle ga haka aka kira ku in kuna jiki guda, ku kuma kasance masu gode wa Allah.


A cikinsa ne ku kuma aka gina ku, ku zama mazaunin Allah ta wurin Ruhu.


yă kuma sulhunta su duka biyu ga Allah, su zama jiki ɗaya ta wurin gicciye, ta haka yă kashe gābar.


Don haka sai ku je ku almajirtar da dukkan al'ummai, kuna yi musu baftisma da sunan Uba, da Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki,


Ya kai, wanda kake begen Isra'ila, Mai Cetonta a lokacin wahala, Ƙaƙa ka zama kamar baƙo a ƙasar? Kamar matafiyi wanda ya kafa alfarwarsa a gefen hanya don ya kwana, ya wuce?


Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami.


Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai Cetonmu, da kuma na Almasihu Yesu abin begenmu,


Da yake gurasar nan ɗaya ce, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama mu duk gurasa ɗaya muke ci.


Don in wani ya zo yana wa'azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa'azi, ko kuma in kun sami wani ruhu dabam da Ruhun da kuka samu, ko wata bishara dabam da wadda kuka yi na'am da ita, ashe, har kuna saurin yin na'am da irinsu ke nan!


Amma mun gaskata, cewa, albarkacin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”


“Mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, Wanda Ubangiji ne madogararsa.


Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi.


Saboda abokaina da aminaina, Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ