Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.
Sa'an nan dukan fādawanka za su zo wurina su fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama'arka!’ Sa'an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir'auna a husace.
Sai ku biya shi hakkinsa a ranar da ya yi aikin, kafin faɗuwar rana, gama shi matalauci ne, zuciyarsa tana kan abin hakkinsa, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har ya zama laifi a gare ku.
Sai Jonatan ya tashi da fushi daga wurin cin abinci, bai ci abinci a rana ta biyu ga watan ba, saboda baƙin ciki a kan Dawuda, domin kuma mahaifinsa ya kunyata shi.