Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Afisawa 4:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Afisawa 4:11
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan ba ku sarakuna waɗanda suke yi mini biyayya da hikima da fahimi.


waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin,


Kai kuwa, sai ka natsu a cikin kowane hali, ka jure wa shan wuya, kana aikin mai bishara, ka cika hidimarka.


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.


Saboda haka, Nassi ya ce, “Sa'ad da ya hau Sama ya bi da rundunar kamammu, Ya kuma yi wa 'yan adam baye-baye.”


wanda a zamanin dā ba a sanar da 'yan adam ba, kamar yadda a yanzu aka bayyana wa manzanninsa tsarkaka da annabawa, ta wurin Ruhu,


in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa,


Isra'ila kuwa ta daɗe ba ta bin Allah na gaskiya, ba ta da firist mai koya mata, ba ta kuma bin shari'a.


Ko da yake kamar a yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba.


Ki yi farin ciki saboda an yi masa haka, ya sama! Ku yi farin ciki, ku tsarkaka da manzanni da annabawa, domin Allah ya rama muku abin da ya yi muku!”


Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa.


To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.


Garun birnin kuwa, tana da dutsen harsashi goma sha biyu, a jikinsu kuma an rubuta sunayen manzannin nan goma sha biyu na Ɗan Ragon.


Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ