Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Afisawa 3:19 - Littafi Mai Tsarki

19 ku kuma san ƙaunar da Almasihu yake yi mana, wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan falala ta Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Afisawa 3:19
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ikkilisiya ita ce jikin Almasihu, cikar mai cika dukkan abu.


domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah.


Ƙaunar Almasihu a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.


Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri.


Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.


An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.


Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.


har ku sami kaifin basira tare da dukan tsarkaka, ku fahimci ko mene ne fāɗin ƙaunar Almasihu, da tsawonta da zacinta, da kuma zurfinta,


Amma ku ƙaru da alherin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, da kuma har abada. Amin! Amin!


Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.


“Albarka tā tabbata ga masu kwaɗaita ga adalci, domin za a biya musu muradi.


Ku maza, ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci ikkilisiya, har ya ba da kansa dominta,


Sa'an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah, Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki, In raira waƙar yabo a gare ka da garayata, Ya Allah, Allahna!


Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.


Zan gan ka domin ni adali ne, Sa'ad da na farka, kasancewarka tana cika ni da farin ciki.


Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi?


ko tsawo, ko zurfi, kai, ko kowace irin halitta ma, ba za su iya raba mu da ƙaunar da Allah yake yi mana ta wurin Almasihu Yesu Ubangijinmu ba.


Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi, kuna farin ciki matuƙa, wanda ya fi gaban ambato,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ