Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Afisawa 3:16 - Littafi Mai Tsarki

16 ina addu'a ya yi muku baiwa bisa ga yalwar ɗaukakarsa, ku ƙarfafa matuƙa a birnin zuciyarku ta wurin Ruhunsa,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Afisawa 3:16
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Allah yă dai ƙarfafa ku da matuƙar ƙarfi bisa ga ƙarfin ɗaukakarsa, domin ku jure matuƙa a game da haƙuri da farin ciki,


Zan iya yin kome albarkacin wannan da yake ƙarfafa ni.


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Zan ƙarfafa su, Za su yi tafiya da sunansa, Ni Ubangiji na faɗa.”


Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al'ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.


Saboda haka ba mu karai ba, ko da yake jikinmu na mutuntaka yana ta lalacewa, duk da haka, ruhunmu a kowace rana sabunta shi ake yi.


A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.


amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.


Allahna kuma zai biya muku kowace bukatarku daga cikin yalwar ɗaukakarsa da take ga Almasihu Yesu.


Ubangiji yana kiyaye jama'arsa, Yakan kiyaye sarkinsa da ya zaɓa, ya kuma cece shi.


Ni kam, a birnin zuciyata, na amince da shari'ar Allah.


Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.


Ka amsa mini sa'ad da na yi kira gare ka, Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.


Nufinsa ne yă bayyana yalwar ɗaukakarsa ga waɗanda ya yi wa jinƙai, wato, waɗanda dā ma ya yi wa tanadin ɗaukaka?


Su ne Allah ya so ya sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al'ummai, asirin nan kuwa shi ne Almasihu a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,


Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’


Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah,


suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe.


Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.


sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali'u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah.


Allah ya yi wannan kuwa domin a zamani mai zuwa ya bayyana yalwar alherinsa marar misaltuwa, ta wajen nuna mana alheri ta wurin Almasihu Yesu.


Wanda yake Bayahude a zuci, ai, shi ne Bayahude. Kaciyar ainihi kuwa a zuci take, wato ta ruhu, ba ta zahiri ba. Irin wannan mutum, Allah ne yake yaba masa, ba ɗan adam ba.


Allah kuwa da dukan ƙarfinsa zai yi gāba da ni? A'a, zai saurara in na yi magana.


shi da yake sa wa kowace kabila ta sama da ta ƙasa suna,


Sona a ƙarfafa musu zuciya, ƙauna tana haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahimta tabbatacciya, da sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ