Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Haikalin Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato, Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon suna.
A waɗannan kwanaki za a ceci mutanen Yahuza, mutanen Urushalima kuwa za su zauna lafiya. Sunan da za su sa wa Urushalima birninsu, shi ne, ‘Adalcinmu Ubangiji ne.’
Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ɓoyayyiyar manna, zan kuma ba shi wani farin dutse, da sabon suna a rubuce a jikin dutsen, ba kuwa wanda ya san sunan, sai wanda ya karɓe shi.’ ”
bayan ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara sur suna taruwa da Ikkilisiya, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bi da suna Kirista.