Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Afisawa 3:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Saboda haka, ina roƙonku kada ku karai da ganin wahalar da nake sha dominku, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Afisawa 3:13
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ku 'yan'uwa, kada ku gaji da yin aiki nagari.


To, a yanzu ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, a jikina kuma ina cikasa abin da ya saura ga wahalar Almasihu, da aka aza mini saboda jikinsa, wato Ikilisiya,


Ko ana wahalshe mu ma, ai, saboda ta'azantuwarku ce, da kuma lafiyarku. Ko ana ta'azantar da mu, ai, saboda ta'azantuwarku ce, wadda take sa ku, ku jure wa irin wuyan nan, da muke sha.


Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al'ummai,


A wannan rana za a ce wa Urushalima, “Kada ki ji tsoro, ke Sihiyona, Kada ki bar hannuwanki su raunana.


Kada mu yi sanyi da yin aiki nagari, don za mu yi girbi a kan kari, in ba mu karai ba.


suna ƙarfafa masu bi, suna yi musu gargaɗi su tsaya ga bangaskiya, suna cewa, sai da shan wuya mai yawa za mu shiga Mulkin Allah.


ya ce musu, ‘Ku ji, ya ku Isra'ilawa, yau kuna gab da kama yaƙi da magabtanku, kada ku karai, ko ku ji tsoro, ko ku yi rawar jiki, ko ku firgita saboda su.


Saboda haka, da yake muna da wannan hidima bisa ga jinƙan Allah, ba za mu karai ba.


Haka ku ma, ya kamata ku yi farin ciki, ku kuma taya ni farin ciki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ