Afisawa 2:13 - Littafi Mai Tsarki13 Amma a yanzu, a cikin Almasihu, ku da dā kuke can nesa, an kawo ku kusa ta wurin jinin Almasihu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu. “Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al'ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al'ummai.