Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Afisawa 2:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Saboda haka, ku tuna dā ku al'ummai ne bisa ɗabi'a, ga waɗanda ake kira masu kaciyar nan kuwa, sukan kira ku marasa kaciya (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Afisawa 2:11
29 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Almasihu ya yi muku ce, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka.


Ku kuma da kuke matattu saboda laifofinku, marasa kaciya ta jiki, Allah ya raya ku tare da Almasihu, ya yafe mana dukkan laifofinmu,


A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.


Ku kuma dā a rabe kuke da Allah, maƙiyansa a zuci, masu mugun aiki.


Don mu ne masu kaciyar ainihi, masu bauta wa Allah ta wurin Ruhu, masu taƙama da Almasihu Yesu, ba mu kuma dogara da al'amuran ganin ido,


domin dā ku duhu ne, amma a yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske,


To, mutanen nan masu son nuna bijinta cikin jiki, su ne masu son tilasta muku yin kaciya, don gudun shan wuya saboda gicciyen Almasihu.


Kun sani fa a sa'ad da kuke bin al'ummai, an juyar da ku ga bin gumakan nan marasa baki yadda aka ga dama.


Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.


Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?”


Ku tuna fa, ku dā bayi ne a Masar, domin haka ku lura, ku kiyaye waɗannan dokoki.


Ku tuna dā ku bayi ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnku ya 'yantar da ku, domin haka nake ba ku wannan umarni yau.


“Tuna fa, kada ku manta da yadda kuka sa Ubangiji Allahnku ya yi fushi a jeji. Tun daga ranar da kuka fita daga Masar har kuka iso wannan wuri kuna ta tayar wa Ubangiji.


Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.


“Mu da aka haifa Yahudawa, ba al'ummai masu zunubi ba,


Sa'an nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau. Za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda muguntarku da ayyukanku na banƙyama.


Ka tuna fa, dā kai bawa ne a ƙasar Masar, amma Ubangiji Allahnka ya fisshe ka da dantse mai iko, mai ƙarfi. Domin haka Ubangiji Allahnka ya umarce ka ka kiyaye ranar Asabar.


A nan za ku tuna da ayyukanku da dukan abubuwa da kuka ɓata kanku da su. Za ku ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata.


Baranka ya taɓa kashe zaki da beyar, wannan arne zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, tun da yake ya raina rundunar Allah mai rai.


In kuwa marar kaciya yana kiyaye farillan Shari'a, ashe, ba sai a lasafta rashin kaciyarsa a kan kaciya ba?


Ashe, wanda rashin kaciya al'adarsa ce, ga shi kuwa, yana bin Shari'ar daidai, ba sai yă kāshe ka ba, kai da kake da Shari'a a rubuce da kuma kaciya, amma kana keta Shari'ar?


Amma in an sassare waɗansu rassan zaitun na gida, kai kuma da kake zaitun na jeji aka ɗaura aure da kai a gurbinsu, kana kuma shan ni'imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,


waɗanda dā kuke a ciki, kuna biye wa al'amarin duniyar nan, kuna bin sarkin masu iko a sararin sama, wato iskar nan da take zuga zuciyar kangararru a yanzu.


Sai suka ce masa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi garkata.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ