Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Afisawa 1:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Shi ne kuwa tabbatawar gādonmu har kafin mu kai ga samunsa, wannan kuma domin yabon ɗaukakarsa ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Afisawa 1:14
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Allah kuwa shi ya tanadar mana wannan sākewar, shi da ya ba mu Ruhunsa, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.


Ya buga mana hatiminsa cewa mu nasa ne, ya kuma yi mana baiwa da Ruhunsa a zukatanmu, domin tabbatar da abin da zai yi a nan gaba.


Ku kuma kula, kada fa ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda aka hatimce ku da shi, cewa ku nasa ne a ranar fansa.


Tun da yake ku 'ya'ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, yana kira, “Ya Abba! Uba!”


Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan.


domin mu da muka fara kafa bege ga Almasihu mu yi zaman yabon ɗaukakarsa.


To, yanzu na danƙa ku ga Ubangiji, maganar alherinsa kuma tă kiyaye ku, wadda ita take da ikon inganta ku, ta kuma ba ku gādo tare da dukan tsarkaka.


Ya kawo su tsattsarkar ƙasarsa, Ya kawo su a duwatsun da shi kansa ya ci da yaƙi.


Ka tuna da jama'arka waɗanda ka zaɓa su zama naka tuntuni, Ka tuna da jama'arka waɗanda ka fansa, Don su zama kabilarka. Ka tuna da Dutsen Sihiyona, inda zatinka yake!


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.


Sa'ad da waɗannan al'amura suka fara aukuwa, sai ku ɗaga kai ku dubi sama, domin fansarku ta yi kusa.”


Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.


A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ