11 Don duk wanda ya yi masa maraba, mugun aikinsa, sai yă shafe shi.
11 Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.
Kada ka yi garajen ɗora wa kowa hannu, kada kuwa zunuban waɗansu su shafe ka. Ka tsare kanka a tsarkake.
Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su.
Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa, “Ku fito daga cikinta, ya ku jama'ata, Kada zunubanta su shafe ku, Kada bala'inta ya taɓa ku.
Sa'ad da kuka ga ɓarawo kukan yi abuta da shi. Kuna haɗa kai da mazinata.
Ai, duk wanda yake nono ne abincinsa, bai ƙware da maganar adalci ba, kamar jariri yake.
kuna ceton waɗansu kuna fizgo su daga wuta. Waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro kuna ƙyamar ko da tufafin da halinsu na mutuntaka ya ƙazantar.