Ka yi fama, famar gaske saboda bangaskiya, ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira ka saboda shi, sa'ad da ka bayyana yarda, kyakkyawar bayyana yarda, a gaban shaidu masu yawa.
Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.
“ ‘Na san ayyukanka. Ka ga, na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka, kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba.
Tun da yake ka kiyaye maganar da na yi maka ta yin jimiri, Ni ma zan kiyaye ka daga sharrin lokacin nan na gwaji, wanda zai auko wa dukan duniya, don a gwada mazaunan duniya.
Yayin da Yahaya ya kusa gama nasa zamani, sai ya ce, ‘Wa kuke tsammani nake? Ba fa ni ne shi ɗin nan ba. Amma ga shi akwai wani mai zuwa a bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in balle ba.’
Da umarnin wahayi ne na tafi, har na rattaba musu bisharar da nake yi a cikin al'ummai, amma a keɓance a gaban waɗansu shugabannin ikkilisiya, kada himmar da nake yi, ko wadda na riga na yi, ta zamana ta banza ce.
Sai aka ba kowannensu farar riga, aka ce musu, su dai huta kaɗan, har a cika adadin abokan bautarsu, wato, 'yan'uwansu, waɗanda za a kashe, kamar yadda su ma aka kashe su.