kada kuma su ɓata zarafinsu a wajen almara da yawan ƙididdigar asali marar iyaka, waɗanda sukan haddasa gardandami, a maimakon riƙon amanar al'amuran Allah da bangaskiya.
Ai, ba tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo muka bi ba, sa'ad da muka sanar da ku ikon Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanarsa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran.
Sukan faɗa wa annabawa su yi shiru. Sukan ce, “Kada ku yi mana magana a kan abin da yake daidai. Ku faɗa mana abin da muke so mu ji ne kawai. Bari mu ci gaba da ruɗewarmu.
Don zuciyar jama'ar nan ta yi kanta, Sun toshe kunnuwansu, Sun kuma runtse idanunsu, Don kada su gani da idanunsu, Su kuma ji da kunnuwansu, Su kuma fahimta a zuciyarsu, Har su juyo gare ni in warkar da su.’