22 Ubangiji yă kasance a zuciyarka. alheri yă tabbata a gare ku.
22 Ubangiji yă zama tare da ruhunka. Alheri yă zama tare da ku.
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.
Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku, 'yan'uwa. Amin.
Ni Bulus, ni nake rubuta gaisuwar nan da hannuna. Ku tuna da ɗaurina. Alheri yă tabbata a gare ku.
Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu. Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.
Alherin Ubangiji Yesu yă tabbata ga dukkan tsarkaka. Amin!
Ku gai da juna da sumbar ƙauna. Salama tă tabbata a gare ku duka, ku na Almasihu.
Alheri yă tabbata ga dukkan masu ƙaunar Ubangijinmu Yesu Almasihu da ƙauna marar ƙarewa.
Waɗansu kuwa, a garin taƙama, da haka har sun kauce wa bangaskiya. Alheri yă tabbata a gare ku.
Alherin Ubangiji Yesu Almasihu, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su tabbata a gare ku duka.
Alherin Ubangijinmu Yesu yă tabbata a gare ku.
Allah mai ba da salama kuwa, zai sa ku tattake Shaiɗan da hanzari. Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku.
kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”
Alherin Ubangiji Yesu Almasihu yă tabbata a zukatanku.