Can ya tarar da wani Bayahude mai suna Akila, asalinsa kuwa mutumin Fantas ne, bai daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, tare da mata tasa Bilkisu, don wai Kalaudiyas ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu.
Ikilisiyoyin ƙasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikkilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku da kyau da kyau saboda Ubangiji.
Sai ya fara wa'azi gabagaɗi a majami'a, amma da Bilkisu da Akila suka ji maganarsa, suka ja shi a jika, suka ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai.
Bulus kuwa da ya ƙara kwanaki da yawa, bayan ya sausaye kansa a Kankiriya don ya cika wa'adin da ya ɗauka, ya yi bankwana da 'yan'uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Bilikisu da Akila.