Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Timoti 4:10 - Littafi Mai Tsarki

10 domin Dimas, saboda ƙaunar duniyar nan, ya yashe ni, ya tafi Tasalonika. Karaska ya tafi ƙasar Galatiya, Titus kuma ya tafi ƙasar Dalmatiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Timoti 4:10
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka dai sani duk waɗanda suke ƙasar Asiya sun juya mini baya, a cikinsu kuwa har da Fijalas da kuma Harmajanas.


duk da haka dai hankalina bai kwanta ba, domin ban tarar da ɗan'uwana Titus a can ba, saboda haka, sai na yi bankwana da su, na zarce na tafi Makidoniya.


Sai suka zazzaga ƙasar Firijiya da ta Galatiya, saboda Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin Maganar Ubangiji a ƙasar Asiya.


haka kuma Markus, da Aristarkus, da Dimas, da Luka, abokan aikina, suna gaishe ka.


A lokacin da na ba da hanzarina na farko, ba wanda ya goyi bayana, sai duk suka yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.


Dukansu sha'anin gabansu kawai suke yi, ba na Yesu Almasihu ba.


Amma Allah, shi da yake ƙarfafa wa ƙasƙantattu zuciya, sai ya ƙarfafa mana zuciya da zuwan Titus,


To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.


To, da suka bi ta Amfibolis da Aboloniya, suka isa Tasalonika, inda wata majami'ar Yahudawa tāke.


Sun yar da miƙaƙƙiyar hanya, sun bauɗe, sun bi hanyar Bal'amu ɗan Beyor, wanda ya cika son samu ta hanyar mugunta.


zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka. Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.


Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.


Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.


da kuma dukan 'yan'uwa da suke tare da ni, zuwa ga ikilisiyoyin ƙasar Galatiya.


Godiya tā tabbata ga Allah wanda ya sa tsananin kula da ku a zuciyar Titus, kamar yadda nake yi.


Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi.


Bayan da ya ɗan jima a nan, ya tashi ya zazzaga ƙasar Galatiya da ta Firijiya, yana bin gari gari, yana ƙarfafa dukan masu bi.


Amma da Yahudawan Tasalonika suka ji labari Bulus yana sanar da Maganar Allah a Biriya ma, suka je suka zuga taro masu yawa a can ma, suna ta da hankalinsu.


Amma Bulus bai ga ya kyautu su tafi da wanda ya rabu da su a ƙasar Bamfiliya, ya ƙi tafiya aiki tare da su ba.


Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafusa a jirgin ruwa, suka isa Bariyata ta ƙasar Bamfiliya. Yahaya kuwa ya bar su, ya koma Urushalima.


Ba baran da zai iya bauta wa iyayengiji biyu, ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗaya, ko kuwa ya amince wa ɗayan, ya raina ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah da dukiya gaba ɗaya.”


Haka ma, kowannenku in bai saki duk abin da ya mallaka ba, ba zai iya zama almajirina ba.”


Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.


Kowa ya aibata Ɗan Mutum, ā gafarta masa. Amma wanda ya aibata Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, duniya da lahira.”


Titus kuwa, ai, abokin tarayyata ne, abokin aikina kuma game da al'amuranku. 'Yan'uwan nan namu kuwa, ai, manzanni ne na ikilisiyoyi, masu ɗaukaka Almasihu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ