7 kullum suna koyo, amma kullum sai su kāsa kaiwa ga sanin gaskiya.
7 kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya.
An yi wannan kuwa don kada mu sāke zama kamar yara, waɗanda suke jujjuyawa, iskar kowace koyarwa tana ɗaukar hankalinsu, bisa ga wayon mutane da makircinsu da kissoshinsu.
wanda yake son dukkan mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya.
Muna da abu da yawa da za mu faɗa a game da shi kuwa, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.
mai sa abokan hamayyarsa a kan hanya da tawali'u, ko Allah zai sa su tuba, su kai ga sanin gaskiya,
Ta yaya za ku ba da gaskiya, ku da kuke karɓar girma a junanku, girman da yake daga Allah Makaɗaici kuwa, ba kwa nemansa?
Mutum mai fāriya ba zai taɓa zama mai hikima ba sam, amma mutum mai basira yakan koya a sawwaƙe.
Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba.
Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba.