Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.
Ya ku 'yan yarana, zamanin ƙarshe ne fa. Kamar yadda kuka ji, magabcin Almasihu yana zuwa, ko a yanzu ma, magabtan Almasihu da yawa sun zo. Ta haka muka sani zamanin ƙarshe ne.
Zai zama nan gaba, dutse inda Haikalin Ubangiji yake Zai zama shi ne mafi tsawo duka a cikin duwatsu, Zai fi tuddai tsayi, Mutane kuwa za su riƙa ɗunguma zuwa wurinsa.
“Tun daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana dubu da ɗari biyu da tasa'in.
Za ka zo ka yi yaƙi da mutanen Isra'ila, za ka rufe su kamar yadda girgije yakan rufe sararin sama. A kwanaki na ƙarshe zan kawo ka ka yi yaƙi da ƙasata domin al'ummai su san ni sa'ad da na bayyana tsarkina a gabansu ta wurin abin da ka yi.’ ”
Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”
“Sa'an nan sarki zai yi yadda ya ga dama. Zai ɗaukaka kansa, ya aza ya fi kowane allah. Zai kuma yi maganganu na saɓo a kan Allahn alloli, zai yi nasara, sai lokacin da aka huce haushi, gama abin da aka ƙaddara zai cika.
Bayan wannan mutanen Isra'ila za su komo su nemi Ubangiji Allahnsu, da Dawuda, sarkinsu. Da tsoro za su komo zuwa wurin Ubangiji domin alheransa a kwanaki na ƙarshe.
Ina duban ƙahonin, sai ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙane, ya ɓullo a tsakiyarsu. Sai aka tumɓuke ƙaho uku na fari daga cikinsu. Wannan ƙaramin ƙaho yana da idanu kamar na mutum, yana kuma da baki, yana hurta maganganu na fariya.”