Saboda haka, kada ka ji kunyar ba da shaidar Ubangijinmu, da kuma tawa, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi, sai dai mu jure wa shan wuya tare, saboda bishara, bisa ga ikon Allah,
da kuma yawan tsanani, da wuyar da na sha, da suka same ni a Antakiya, da Ikoniya, da Listira, wato irin tsanance-tsanancen da na jure. Amma Ubangiji ya kuɓutar da ni daga cikinsu duka.
Ko ana wahalshe mu ma, ai, saboda ta'azantuwarku ce, da kuma lafiyarku. Ko ana ta'azantar da mu, ai, saboda ta'azantuwarku ce, wadda take sa ku, ku jure wa irin wuyan nan, da muke sha.