Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Timoti 2:18 - Littafi Mai Tsarki

18 waɗanda suka bauɗe wa gaskiya suna cewa tashin matattu ya riga ya wuce, suna jirkitar da bangaskiyar waɗansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Timoti 2:18
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

To, da yake ana wa'azin Almasihu a kan an tashe shi daga matattu, ƙaƙa waɗansunku suke cewa, babu tashin matattu?


kana riƙe da bangaskiya da lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.


Saboda haka ne, na yi fushi da mutanen wannan zamani, Har na ce, ‘A kullum zuciyarsu a karkace take, Ba su kuwa san hanyoyina ba.’


Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.


Ya ku 'yan'uwana, in waninku ya bauɗe wa gaskiya, wani kuma ya komo da shi,


Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.


Waɗansu kuwa, a garin taƙama, da haka har sun kauce wa bangaskiya. Alheri yă tabbata a gare ku.


Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.


To, da yake an tashe ku tare da Almasihu, sai ku nemi abubuwan da suke a Sama, inda Almasihu yake, a zaune a dama ga Allah.


Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.


amma in na Allah ne, ba dama ku rushe su. Kada fa a same ku kuna gāba da Allah.”


Na kan dutsen kuwa su ne waɗanda da zarar sun ji Maganar, sai su karɓa da farin ciki. Su kam, ba su da tushe. Sukan ba da gaskiya 'yan kwanaki kaɗan, amma a lokacin gwaji, sai su bauɗe.


Amma Yesu ya amsa musu ya ce, “Kun ɓăta ne, domin ba ku san Littattafai ba, ba ku kuma san ikon Allah ba.


Ya amsa ya ce, “Duk dashen da ba Ubana da yake Sama ne ya dasa ba, za a tumɓuke shi.


Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama'a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ