Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Timoti 2:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Ka yi nesa da masu maganganun banza na sāɓo. Sai daɗa jan mutane zuwa ga rashin bin Allah suke yi,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Timoti 2:16
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ka yi nesa da gardandamin banza, da ƙididdigar asali, da husuma, da jayayya a kan Shari'a, domin ba su da wata riba, aikin banza ne kuma.


Ya Timoti, ka kiyaye abin da aka ba ka amana. Ka yi nesa da masu maganganun sāɓo na banza da wofi, da yawan musu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi.


a maimakon su mai da hankali ga almarar Yahudawa, ko kuwa dokokin mutane masu ƙin gaskiya.


Ka riƙa tuna musu da haka, ka kuma gama su da Ubangiji, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.


Ifraimu tana kiwon iska, Tana ta bin iskar gabas dukan yini. Tana riɓaɓɓanya ƙarya da kamakarya. Tana ƙulla yarjejeniya da Assuriya, Tana kai mai a Masar.”


Ezra firist kuwa ya miƙe tsaye ya ce wa jama'a, “Kun yi rashin aminci, kun auri mata baƙi, ta haka kuka ƙara zunubin Isra'ila.


Ɗaya daga cikin kawunanta, an yi masa rauni kamar na ajali, amma rauninsa mai kamar na ajalin nan ya warke. Sai dabbar ta ɗauke wa duk duniya hankali, suna mamaki,


Ta surutai barkatai marasa kan gado na ruba, da halinsu na fasikanci sukan shammaci waɗanda da ƙyar suke kuɓucewa daga masu zaman saɓo,


Da yawa kuwa za su bi fajircinsu, har za a kushe hanyar gaskiya saboda su.


Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,


Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama'a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.


Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.


Ka ƙi tatsuniyoyin saɓo da na banza da wofi. Ka hori kanka ga bin Allah.


Kada fa a yaudare ku! “Zama da mugaye yakan ɓata halayen kirki.”


Fāriyarku ba shi da kyau. Ashe, ba ku sani ba, ɗan yisti kaɗan yake game dukkan curin gurasa?


Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al'ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.


yana kuma tunawa, cewa ita Shari'a ba a kafa ta domin masu adalci ba, sai dai kangararru, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai,


Kowa yă tsarkake kansa daga ayyukan nan ƙasƙantattu, zai zama ma'aikaci mai daraja, tsarkakakke, mai amfani ga Ubangiji, shiryayye ga kowane kyakkyawan aiki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ