Duk da haka yanzu sai ku yi ƙarfin hali, kai Zarubabel, da kai Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukanku mutanen ƙasar, ku kama aikin, gama ina tare da ku. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
Ka dai dāge, ka yi ƙarfin hali ƙwarai, kana kiyaye dukan dokokin da bawana Musa ya umarce ka da su. Kada ka kauce musu dama ko hagu, gama da haka nan za ka arzuta cikin dukan harkokinka.