Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Timoti 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Sa'ad da nake tunawa da hawayenka, nakan yi began ganinka dare da rana, domin in yi farin ciki matuƙa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Timoti 1:4
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo wurina da hanzari,


Ka yi matuƙar ƙoƙari ka zo kafin damuna. Aubulus yana gaishe ka, da Budis, da Linas, da Kalaudiya, da kuma dukkan 'yan'uwa.


Ya ku 'yan'uwa, ko da yake mun yi kewarku saboda an raba mu a ɗan lokaci kaɗan, duk da haka kuna cikin zukatanmu, mun kuwa ƙara ɗokanta mu gan ku ido da ido, matuƙar ɗoki.


Domin Allah shi ne mashaidina a kan yadda nake begenku duka, da irin ƙaunar da Almasihu Yesu yake yi.


zai share musu dukkan hawaye. Ba kuma sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba, don abubuwan dā sun wuce.”


domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”


Muna kuma rubuto muku wannan ne domin farin cikinmu ya zama cikakke.


Yana begenku ku duka, har ma ya damu ƙwarai don kun ji ba shi da lafiya.


Domin ina ɗokin ganinku, in ni'imta ku da wata baiwa ta ruhu, domin ku ƙarfafa.


Saboda haka sai ku zauna a faɗake, ku tuna, shekara uku ke nan ba dare ba rana, ban fasa yi wa kowa gargaɗi ba, har da hawaye.


ina bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali'u, har da hawaye, da gwaggwarmaya iri iri da na sha game da makircin Yahudawa.


Har yanzu dai ba ku roƙi kome da sunana ba. Ku roƙa, za ku samu, domin farin cikinku ya zama cikakke.”


Haka ku ma yanzu kuke tare da baƙin ciki, amma zan sāke ganinku, sa'an nan zuciyarku za ta yi fari, ba kuwa mai ɗauke muku farin cikinku.


Sa'an nan 'yan mata za su yi rawa da farin ciki, Samari da tsofaffi za su yi murna. Zan mai da makokinsu ya zama murna, Zan ta'azantar da su, in ba su farin ciki maimakon baƙin ciki.


Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi.


Ka sa waɗanda suke kuka a lokacin da suke dashe, Su tattara albarkar kaka da farin ciki!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ