11 A wannan bishara an sa ni mai wa'azi, da kuma manzonta, da mai koyarwarta kuma.
11 A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami.
Don haka ne aka sa ni mai wa'azi, da manzo kuma (gasikya nake faɗa, ba ƙarya ba), mai koya wa al'ummai al'amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.
Amma Ubangiji ya ce masa, “Kai dai, je ka, domin shi ma'aikacina ne zaɓaɓɓe, domin yă sanar da sunana ga al'ummai, da sarakuna, da kuma Isra'ilawa.
Suna burin zama masanan Attaura, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle matsalar da suke taƙamar haƙiƙicewa a kai.
Ni ba ɗa ba ne? Ba kuma manzo ba ne? Ban ga Yesu Ubangijinmu ba ne? Ku ba aikina ba ne a cikin Ubangiji?