Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tessalonikawa 3:2 - Littafi Mai Tsarki

2 a kuma cece mu daga fanɗararrun mutane, mugaye. Don ba duka ne suke da bangaskiya ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tessalonikawa 3:2
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin in tsira daga maƙiyan bangaskiya a Yahudiya, don kuma gudunmawar da nake kaiwa Urushalima, ta zama abar karɓa ga tsarkaka,


Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata, Zan ga yadda ƙarshensu zai zama. Gama su muguwar tsara ce, 'Ya'ya ne marasa aminci.


Amma ba duka ne suka yi na'am da bisharar ba. Ishaya ma ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?”


Waɗansu sun rinjayu da maganarsa, amma waɗansu sun ƙi gaskatawa.


Mun dai yi niyyar zuwa wurinku, ni Bulus, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, amma Shaidan ya hana.


Amma Yahudawa da suka ƙi bi, suka zuga al'ummai, suka ɓata tsakaninsu da 'yan'uwa.


Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu ibada, masu daraja, da kuma waɗansu manyan gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu.


Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa.


Ina gaya muku, zai biya musu hakkinsu, da wuri kuwa. Amma kuwa sa'ad da Ɗan Mutum ya zo, zai tarar da bangaskiya a duniya ne?”


“Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan fitar da zakkar na'ana'a, da anise, da lafsur, amma kun yar da muhimman jigajigan Attaura, wato, gaskiya, da jinƙai, da aminci. Waɗannan ne ya kamata ku yi, ba tare da yar da sauran ba.


Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”


Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al'ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.


Idan bisa ga ra'ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?”


Amma Yahudawa, saboda kishi, suka ɗibi waɗansu ashararai, 'yan iska, suka tara jama'a suka hargitsa garin kaf, suka fāɗa wa gidan Yason, suna nemansu don su fito da su gaban taron jama'a.


Don ni, a ganina, wauta ce a aika da ɗan sarƙa, ba tare da an nuna laifofin da ya yi ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ