Kun kuma mance da gargaɗin nan da Allah ya yi muku a kan ku 'ya'yansa ne, wato “Ya ɗana, kada ka raina horon Ubangiji, Kada kuma ka karai, in ya kwaɓe ka.
Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,
Kuka kuma ce, ‘Mun gaji da wannan irin abu fa!’ Kuna hura mini hanci. Kukan kawo satacciyar dabba, ko gurguwa ko marar lafiya, ku yi mini hadaya da ita! Kuna tsammani zan karɓi wannan daga gare ku?
“Shugabannin yaƙi za su ci gaba da yi wa jama'a magana, su ce, ‘Ko akwai wani mutum a nan wanda yake jin tsoro, wanda zuciyarsa ta karai? Sai ya koma gidansa don kada ya sa zuciyar sauran 'yan'uwansa kuma su karai.’
Sa'ad da kuma aka sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa ɗin, sa'an nan ne Ɗan da kansa shi ma zai sarayar da kansa ga wannan da ya sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa, domin Allah yă tabbata shi ne kome da kome.