Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”
Don hukuncinsa daidai yake, na adalci ne, Ya hukunta babbar karuwar nan wadda ta ɓata duniya da fasikancinta, Ya kuma ɗauki fansar jinin bayinsa a kanta.”
Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna, Za su yi māye, da kisankai, da fushi. Sa'an nan dukan 'yan adam za su sani, ni ne Ubangiji, Wanda ya cece ku, ya fanshe ku. Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila.”
Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, Ya kuma ɗaukaka sunanka? Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki. Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada, Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”
Al'ummai sun husata, fushinka kuwa ya auko, Lokaci ya yi da za a yi wa matuttu shari'a, A kuma yi wa bayinka, annabawa da tsarkaka sakamako, Da masu jin tsoron sunanka, yaro da babba, A kuma hallaka masu hallaka duniya.”
“Ku kirawo 'yan baka, dukan waɗanda sukan ja baka, su faɗa wa Babila. Ku kafa sansani kewaye da ita, kada ku bar kowa ya tsira. Ku sāka mata bisa ga dukan ayyukanta, gama ta raina Ubangiji Mai Tsarki na Isra'ila.