2 Tarihi 9:9 - Littafi Mai Tsarki9 Sa'an nan kuma ta ba sarki zinariya talanti ɗari da ashirin, da kayan yaji masu yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Irin kayan yajin da Sarauniyar Sheba ta ba sarki Sulemanu ba irinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da 'yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta.