Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 9:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda yake murna da kai, wanda ya hawar da kai gadon sarautarsa, don ka zama sarki a gaban Ubangiji Allahnka. Gama Allah yana ƙaunar Isra'ila, zai kuwa tabbatar da su har abada, shi ya sa ya naɗa ka sarkinsu, don ka aikata gaskiya da adalci.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 9:8
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hiram, Sarkin Taya kuwa, ya ba Sulemanu amsar takardarsa, ya ce, “Saboda Ubangiji yana ƙaunar jama'arsa, ya naɗa ka sarkinsu.”


Sai Sulemanu ya zauna a kan gādon sarauta na Ubangiji maimakon tsohonsa Dawuda. Ya yi nasara a cikin sarautar, Isra'ilawa dukansu suka yi masa biyayya.


Amma saboda Ubangiji ya ƙaunace ku, yana kuma so ya cika rantsuwar da ya yi wa kakanninku, shi ya sa ya fisshe ku da dantse mai iko ya fanshe ku kuma daga gidan bauta, wato daga ikon Fir'auna, Sarkin Masar.


Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


Ubangiji ya fi so ka yi abin da yake daidai, mai kyau kuma, fiye da ka miƙa masa hadayu.


Maɗaukaki kana ƙaunar abin da yake daidai, Ka kawo adalci cikin Isra'ila, Ka kawo adalci da gaskiya.


Don ya yi mulkin jama'arka bisa kan shari'a, Ya kuma bi da mulki da adalci.


Suka ce, “Ka dogara ga Ubangiji, Me ya sa bai cece ka ba? Idan Ubangiji na sonka, Don me bai taimake ka ba?”


Ya fisshe ni daga cikin hatsari, Ya cece ni, don yana jin daɗina.


Sa'an nan Dawuda ya ce wa taro duka, “Sai ku yabi Ubangiji Allahnku yanzu.” Taron jama'a kuwa suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu, suka rusuna har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada, suka kuma girmama sarki.


Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na kakanmu Yakubu, yabo ya tabbata gare ka har abada abadin!


Daga cikin dukan 'ya'yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni 'ya'ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra'ila, abin mulkin Ubangiji.


Gama ka mai da jama'ar Isra'ila ta zama taka har abada. Kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.


Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda ya yarda da kai, ya sa ka a kan gadon sarautar Isra'ila, domin Ubangiji yana ƙaunar Isra'ila har abada, ya naɗa ka sarki domin ka zartar da shari'a da adalci.”


Sa'ad da dukan mutanen Isra'ila suka ji shari'ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.


Allah na Isra'ila ya yi magana, Matsaron Isra'ila ya ce mini, ‘Sarkin da yake mulkin mutane da adalci, Wanda yake mulki da tsoron Allah,


Dawuda ya mallaki Isra'ila duka. Ya yi wa dukan jama'arsa shari'ar gaskiya da adalci.


Ba za a ƙara ce da ke, “Yasasshiya” ba, Ko a ce da ƙasarki, “Mata wadda Mijinta ya Rabu da Ita.” Sabon sunanki yanzu shi ne, “Wadda Allah ya Yarda da Ita.” Ƙasarki kuwa za a ce da ita, “Ta yi Aure da Farin Ciki,” Domin Ubangiji ya ji daɗinki, Zai kuwa zama kamar miji ga ƙasarki.


Ubangiji ya ce, “Ga bawana, wanda na ƙarfafa, Wanda na zaɓa, wanda nake jin daɗinsa. Na cika shi da ikona, Zai kuwa kawo shari'ar gaskiya ga dukan al'ummai.


Masu farin ciki ne mutanenka, da barorinka waɗanda suke yi maka hidima kullayaumin, gama kullum suna jin hikimarka.


Sa'an nan kuma ta ba sarki zinariya talanti ɗari da ashirin, da kayan yaji masu yawan gaske, da duwatsu masu daraja. Irin kayan yajin da Sarauniyar Sheba ta ba sarki Sulemanu ba irinsa.


Sarkin da yake aikata adalci ƙasarsa za ta yi ƙarƙo, amma wanda yake karɓar rashawa zai lalatar da ƙasar.


Zan ba barorinka masu aikin katako misalin mudu dubu ashirin (20,000) ta sussukakkiyar alkama, da mudu dubu ashirin (20,000) ta sha'ir, da misalin garwar ruwan inabi dubu ashirin (20,000), da ta mai dubu ashirin (20,000).”


Yanzu kuma, so kuke ku ƙi mulkin Ubangiji wanda yake hannun 'ya'yan Dawuda, maza, saboda yawan da kuke da shi, da gumakan maruƙan zinariya da kuke da su, waɗanda Yerobowam ya yi muku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ