Waɗanda suka tafi Masar neman taimako, sun shiga uku! Suna dogara ga ƙarfin tulin dawakan Masar na yaƙi, da karusansu, da sojojinsu. Amma ba su dogara ga Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila ba, ba su ko roƙe shi taimako ba.
Sulemanu kuwa yana da ɗakunan dawakai da na karusai dubu huɗu (4,000), yana da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000) waɗanda suke zaune a biranen karusai, waɗansu kuma a Urushalima tare da sarki.
suka kuma shigo da karusai daga Masar. Suka riƙa sayar wa sarakunan Hittiyawa da na Suriyawa karusai a kan azurfa ɗari shida shida, kowane doki kuma a kan azurfa ɗari da hamsin.