2 Tarihi 9:2 - Littafi Mai Tsarki2 Sulemanu kuwa ya amsa dukan tambayoyin da ta yi masa, ba wani abu da yake ɓoye ga Sulemanu wanda ya kāsa bayyana mata. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Solomon ya amsa dukan tambayoyinta; babu wani abin da ya yi masa wuya yă bayyana mata. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da 'yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta.