2 Tarihi 9:1 - Littafi Mai Tsarki1 Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da 'yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |